Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Kasashen uku sun sha alwashin yin aiki tare domin samar da mafita ga halin da Lebonan ke ciki.
Saudiyya da Faransa, sun ce sun damu akan samar da tsaro da kuma kwanciyar hankali a Lebanon.
A jiya ne shugaban na faransa ya isa birnin Djeddah, inda ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya, MBS a ziyarar kwanaki biyu a kasashen larabawan yankin Golf.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama sun soki ganawar da Macron ya yi da yariman na Saudiyya, wanda suke dangantawa da mai zubar da jini, sakamakon bankado sunan shi dumu-dumu a kisan dan jarinan nan Jamel Khashoggi.
Kafin Saudiyya, Macron ya je Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma Qatar.
342/